1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Guinea Bissau sun kwace makamai

Suleiman Babayo ZMA
December 7, 2023

A kasar Guinea Bissau da ke yankin yammacin Afirka, sojoji gwamnatin kasar sun nuna makaman da aka yi amfani da su wajen yunkurin juyin mulki.

https://p.dw.com/p/4Zt9b
Makaman da sojojin Guinea Bissau suka kwace daga hanun mahara
Makaman da sojojin Guinea Bissau suka kwace daga hanun maharaHoto: DW

Rundunar sojan kasar Guinea Bissau ta nuna makamai masu sarrafa kansu da rokoki gami da albarusai da ta bayyana cewa an samu daga wadanda ake zargin da yunkurin juyin mulki cikin makon jiya a kasar da ke yankin yammacin Afirka.

Shugaban rundunar sojojin kasar Janar Biague Na Ntam wanda yake ci gaba da biyayya ga gwamnatin, ya nuna makaman da aka kama a birnin Bissau fadar gwamnatin kasar.

Shi dai Shugaba Umaro Sissoco Embalo na kasar ta Guinea Bissau yana birnin Dubai an Hadaddiyar Daular Larabawa inda yake halartar taron sauyin yanayi na duniya da ake kira COP28.