1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun ECOWAS ta kori karar sojojin Nijar

Uwais Abubakar Idris LMJ
December 7, 2023

Kotun kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO, ta yi watsi da karar da gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar da wasu mutane tara suka shigar a gabanta.

https://p.dw.com/p/4Ztq8
Najeriya, birnin Abuja | Taron Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS/CEDEOA
Tun bayan juyin mulki a Nijar din, ECOWAS ke ta kokarin dawo da zababbiyar gwamnatiHoto: Gbemiga Olamikan/AP/picture alliance

Gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar da mutanen tara dai, na bukatar kotun ta kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO ta tilastawa shugabanin kungiyar su dage takunkumin da suka kakabawa kasar bayan juyin mulkin da sojojin suka yi. Wannan shari'a ta dauki hankali sosai a Najeriyar da Jamhuriyar Nijar, abin da ya sanya daukan lokacin da alkalan kotun karkashin jagorancin mai shari'a Dupe Atoki suka yi wajen bayyana dalilan da suka sa su daukar wannan mataki.

Karin Bayani: Bazoum ya yi nasara a kotun Ecowas

Alkalan sun bayyana cewa koda yake Jamhuriyar Nijar kasa ce cikin mabobin ECOWAS ko CEDEAO din, amma gwamnatin mulkin soja da ke kasar ba halastaciyya ba ce. A dangane da haka ne kotun ta ce gwamnatin mulkin sojan Nijar din ba ta da hurumin zuwa gabanta ta kalubalanci matakin da kungiyar ta dauka na saka takunkumi ga kasar takunkumi. A cewar kotun kungiyar ta haramta sauya mulki ta hanyara da ta sabawa tsarin mulki, domin haka ta yi watsi da karar tun da sojojin sun karbe  mulkin ne ta hanyar kifar da halastacciyar gwamnatin farar hula da al'ummar Nijar din suka zaba.

Burkina Faso: Abinci zuwa Nijar

Da kotun ta juya a kan daya bangaren shari'ar na kungiyoyin farar hula da suka shigar tare da gwamnatin kan cewa takunkuman da aka sakawa kasar sun haifar da wahalhalu ga bangaren tattalin arziki da kula da lafiya da ma zamantakewar al'umma, alkalin kotu ta ce koda yake suna da 'yancin shigar da karar a kan lamarin amma zargi ne kawai kungiyoyin da ke rajin kare hakkin al'umma suke yi. A cewar kotun kungiyoyin ba su nuna zahirin shaidar hakan ba, domin haka ta yi watsi da karar tasu.

Karin Bayani: ECOWAS ta ce dakaru su kasance cikin shiri

Tuni dai al'ummar Njijar da ke Najeriyar da suka sanya idannu a kan sakamakon shari'ar, suka fara bayyana ra'ayoyinsu kan yadda shari'ar ta kaya. Wannan hukuncin da kotun kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO ta yanke dai, zai kara haifar da sarkakiya a kan rikicin siyasar Jamhuriyar Nijar din musamman ma da hukuncin ya zo a daidai lokacin da ake jiran taron da shugabannin kasashen kungiyar za su yi a karshen makon nan a Abuja fadar gwamnatin Tarayyar Najeriyar.