1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci daukar mataki kan Isra'ila

December 7, 2023

Sakatare Janar na MDD Antonia Gutterres, ya bukaci amfani da daftarin doka mai lamba 99 da ta bawa kwamitin tsaro ikon gargadin Isra'ila kan barazanar jin kai a Gaza.

https://p.dw.com/p/4Zrqj
USA UN-Sicherheitsrat | Sitzung über den Konflikt zwischen Israel und der Hamas
Hoto: David Dee Delgado/REUTERS

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya  Antonia Gutterres, ya bukaci amfani da daftarin doka mai lamba 99 da ta bawa kwamitin tsaro na majalisar ikon gargadin Isra'ila kan barazanar jin kai a Gaza, inda ya ce yakin na ci gaba da lakume rayukan al'umma.

Kalaman Gutterres na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Isra'ila ke ci gaba da zazzaga bama-bamai a yankin naGaza. Ma'aikatar lafiyar yankin ta ce asibitin Al-Ahli dake Gaza ta yi cikar-kwari da wadanda suka ji munanan raunuka.

Akalla Falasdinawa dubu 16,248 ne suka kwanta dama tun bayan kaddamar da farmakin Isra'ila da Hamas a ranar 7 ga watan Octoba.

A gefe guda, ma'aikatar tsaron Isra'ila ta sanar da cewa sojinta guda biyu sun mutu a yayin fafatawa da mayakan Hamas, sai dai Wasu bayanan Majalisar Dinkin duniya sun tabbatar da mutuwar sojin Isra'ila 88 a yakin.

Hukumar bada agajin gaggawa ta Red Crescent ta sanar da cewa akalla baki 400 dake dauke fasfunan kasashen waje sun bar yankin na Gaza, inda suka tsallaka Masar.